Kakakin ya ce, Sin ta nace ga bin hanyar zaman lafiya da samun bunkasuwa, da tsayawa kan manufar tsaro ta kare kanta, kuma dalilin da ya sa Sin ta inganta harkokin tsaro da karfin soji shi ne domin tabbatar da cin gashin kai da cikakken yankin kasar, da kiyaye tsaron kasar, ba wai domin wata kasa ba.
Geng Yansheng ya ce, a cikin 'yan shekarun nan, Japan ta inganta karfin soji, kuma ta kara jibge soji a tsibiran da ke yammaci da kudancin kasar, kuma an kawo halin kunci tsakaninta da sauran kasashen da ke makwabtaka da ita game da cikakken yankin kasar, kuma hakan ya jawo hankali da damuwa daga kasashen da ke Asiya da tekun Fasific da dama, kasar Sin tana fatan Japan za ta yi tuba game da manufar tsaro ta kasarta, da ci gaba da gudanar da matakan da za su kawo amincewar juna tsakaninta da kasashe makwabtaka, don tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin.(Bako)