in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta bayar da kundin zirga-zirga a cikin sararin samaniya na shekara ta 2011.
2011-12-29 16:14:05 cri

A ranar 29 ga wanan wata,Ofishin watsa labaru na majalisar gudanarwa ta kasar Sin, ya baiyana bayar da kundin ayyukan zirga-zirga a cikin sararin samaniya na shekarar 2011. Wanda ya bayyana cewa, kasar Sin ta na son kiyaye zaman lafiya da tabbatar da tsabta a cikin sararin samaniya, tare da gamayyar kasashen duniya domin kara bada gundummawa wajen neman samun bunkasar dan Adam.

Badda wannan kundi shi ne karo na 3 da gwamnatin kasar Sin ta yi game da aikin zirga-zirga a cikin sararin samaniya, ya kuma kunshi babi-babi guda 6 wato ya kunshi ka'idoji ta fanin bunkasawa, sakamakon da aka samu bayan shekarar ta 2006, babbar dawainiya a shekaru 6 masu zuwa, manufofi da matakai da aka tsara da kuma hadin gwiwa da musayar ra'ayi a tsakanin kasa da kasa. Gwamnatin kasar Sin ta maida aikin zirga-zirga a cikin sararin samaniya a matsayin muhimmin aiki na raya kasar domin yin amfani da sararin samaniya yadda ya kamata.

Bugu da kari, kundin ya bayyana cewa, a cikin shekaru biyar masu zuwa, kasar Sin za ta fuskanci sabon zarafi a fannin zirga-zirgar sararin samaniya, za ta kara kirkiro da sabbin kayayyaki da fasahohi da karfafa yin hadin gwiwa tare da kasashen waje. A lokaci daya kuma, kasar Sin tana son kiyaye zaman lafiya da tabbatar da tsabta a cikin sararin samaniya.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China