Bisa kididdiga dai wannan sanarwa ta ce, yawan makamashi da kasar ta Sin ke amfani da shi na karuwa da kaso 5.82 a kowace shekara, tun daga shekarar 1981 ya zuwa bara, al'amarin dake nuni ga karfafar tattalin arzikin kasar da kaso 10 bisa dari a kowace shekara.
Har ila yau, sanarwar tace Sin ta gina kyakkyawan tsarin samar da makamashin Kwal, da lantarki, da na albarkatun man-fetur, baya ga makamashin iskar Gas da ragowar nau'oin makamashi mai tsafta. Wannan tsari a cewar sanarwar ya kawo sauyi mai nagarta, a fagen bunkasar amfanin da al'umma ke yi da nau'o'in makamashi daban-daban, tun daga lokacin da kasar ta zartas da sabbin manufofin ta, ciki hadda bude kofarta a karshen shekarar 1970. (Saminu Alhassan Usman)