A cikin takardun bayyanai, an jaddada cewa, kasar Sin tana nacewa ga bin ra'ayoyin nuna amincewa juna da moriyar juna da adalci da yin hadin gwiwa, tana son warware batutuwan duniya ta hanyar zaman lafiya, da nuna adawa da aikin karfin tuwo, da adawa da kasar da ke neman shimfida ikonta ba.
A cikin takardun bayyanai, an kara da cewa, bisa bunkasuwar tattalin arzikin kasar Sin, kudin da ake kashewa kan harkokin soja na kasar Sin ya karu.
Ban da haka kuma, an ce, a matsayin wata membar kwamitin sulhu na M.D.D, kasar Sin tana kokarin shiga aikin kiyaye zaman lafiya da M.D.D ta shirya, da yin hadin gwiwa tare da sojojin kasashen waje, da ba da gudumawa ga tabbatar da zaman lafiya a duniya.(Abubakar)