Madaba'ar jama'ar kasar Sin ta buga "Littafin jerin takardun bayanai na gwamnatin kasar Sin na shekarar 2012", kuma an buga su cikin Turanci da fara sayar da su daga yau a duk kasar.
Wadannan takardu na kunshe da takardun bayanai biyar da gwamnatin kasar Sin ta bayar a shekarar 2012, wato "Halin da Sin ke ciki a fannin karfen rare-earth da manufofinta dangane da wannan fanni", da "Tsibirin Diaoyu na karkashin mallakar kasar Sin", da "Kwaskwarimar da Sin ke yi kan batun shari'a", da"Matakan da Sin ta dauka dangane da makamashi na shekarar 2012", da kuma " Sha'anin kiwon lafiya na kasar Sin".
Wadannan takardu sun bayyana matsayi da kuma matakan da Sin ta dauka kan wasu manyan batutuwa, ciki hadda karfen `rare-earth`, tsibirin Diaoyu, kwaskwarima a fannin shari'a, makamashi, da samun tabbaci ga lafiyar jikin Sinawa, da ma ci gaban da Sin ta samu a wasu muhimman bangarori. (Amina)