in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasashen gabashin Afrika na shawarwari domin kawar da cutar malaria nan da shekarar 2015
2013-04-16 10:30:35 cri

Manyan jami'ai na hukumomin tsare-tsaren kasa kan yaki da cutar zazzabin cizon sauro na kasashe 13 dake gabashin Afrika da kuma kwararru na yin wani zaman taron da aka bude tun ranar Litinin a birnin Bujumbura, babban birnin kasar Burundi. A tsawon kwanaki uku, mahalarta wannan taron za su fitar da wani jadawalin aiki da zai taimaka wajen cimma manufar hana mutuwar mutune bisa dalilin cutar malaria nan da shekarar 2015. Haka zalika kuma mahalarta taron za su yi musanyar ra'ayoyi kan daidaita sakamakon bincike tare da bukatun tsare-tsaren kasa na yaki da zazzabin cizon sauro a duk shiyyar gabashin nahiyar Afrika. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China