in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane miliyan 100 za su samu rigakafin cutar sankarau a Afirka
2012-12-04 10:14:21 cri

Cibiyar ba da rigakafin cuta ta kasa da kasa GAVI ta bayyana cewa, mutane miliyan 100 ne a arewacin najeriya wace ta kasance cikin yankin Afirka dake fama da cutar sankarau za su samu wani sabon rigakafin cutar sankarau, yayin da kasar ke gangamin wayar da kai a kan cutar.

Najeriya za ta yi wa mutane miliyan 16 allurar rigakafin cikin makonni biyu masu zuwa, sannan kasashen Cameroun da Chadi su ma suna kan gudanar da gangamin wayar da kai a wannan mako, inda suke sa ran bai wa mutane miliyan 5.5 da kuma miliyan 2.3 rigakafin daki daki, in ji cibiyar ta GAVI cikin sanarwa da ta bayar.

Cibiyar ta ce, daga yanzu zuwa karshen shekarar nan, mutane a kalla miliyan 112 'yan shekaru tsakanin 1 zuwa 29 za su karbi rigakafin don kare su daga cutar, wato tun daga lokacin da aka fara bullo da shirin a shekarar 2010 a Burkina Faso, ta hanyar hadin gwiwa tsakanin kafofin gwamnati da masu zaman kansu da nufin bunkasa lafiya ta hanyar samar da karin damar samun rigakafi a kasashe masu tasowa.

Kasashe guda goma har da Burkina Faso, Mali, Nijar, Najeriya, Chadi, Cameroun, Sudan,Ghana, Benin, da Senegal dukkansu sun yi shirin gangamin wayar da kan jama'a da ba da rigakafin cutar tun lokacin da aka bullo da shirin a 2010.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China