in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yammacin Afrika na fuskantar hadarin yaduwar cutar kwalara, in ji hukumar kiwon lafiya ta duniya
2012-09-06 14:41:51 cri

Hukumar kiwon lafiya ta duniya da asusun tallafawa kananan yara na majalisar dunkin duniya UNICEF sun bayyana cewa, dukkan yanayi wato ruwan sama da ambaliyar ruwa sun hadu domin baiwa cutar kwalara damar yaduwa cikin sauri a yammacin nahiyar Afrika, lamarin da zai kara halin tsanancewar zaman rayuwa a wannan shiyya. Tuni a cikin wannan shekara aka gano kusan nau'in cutar 55.289 a cikin kasashe goma sha biyar tare da mutuwar mutane 1.109.

Annobar ta bazu cikin sauri a cikin kasashen dake yankin kogin Mano da suka hada da Guinee, Laberia da Sierra Leone da kuma a kan tsawon kogin Congo, idan cutar ta shafi al'ummomin kasashen Congon biyu da kuma yammacin Afrika.

Adadin sabbin nau'o'in cutar ya karu cikin sauri a cikin kasashen da suka samu ruwan sama na musammun a wannan shekara wadanda suka janyo ambaliyar ruwa a cikin unguwannin na wasu manyan biranen kasashen.

Yawan nau'in cutar kwalara a yammacin Afrika da tsakiyar Afrika har zuwa wannan lokaci ya karu da kashi 34 cikin 100 idan aka kwatanta da na makamancin lokacin shekarar 2011. Haka kuma adadin mutuwa na iyar cimma kashi 8 cikin 100 lamarin da ya nuna haurawar musamman a wannan shekara. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China