Mr. Zhong ya ce, a cikin 'yan shekarun nan, dangantakar tsakanin kasashen Sin da Ghana ta bunkasa cikin armashi, kuma hadin gwiwa daga dukkan fannoni a tsakaninsu ya habaka cikin hanzari, kuma jama'ar kasashen biyu sun samu alfanu daga cikinsu, tare da fatan ganin an kara zurfafa hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu.
Teteh ta bayyana cewa, bayan da aka kafa dangantakar diplomasiyya tsakanin kasashen Ghana da Sin a cikin shekaru sama da 50 da suka gabata, Sin ta samar da taimako maras jin kai gami da nuna goyon baya ga kasar Ghana, musamman ma a cikin shekarun nan da ake ciki, Sin ta taka muhimmiyar rawa wajen gina muhimman kayayyakin more rayuwa a Ghana, abin da ya ba da babbar gudummawa wajen raya zamantakewar al'umma da tattalin arziki na wurin.(Bako)