A ranar Juma'ar makon nan ne shugaba John Evans Atta Mills na kasar Ghana, ya bayyana bukatar samun hadin kai tsakanin hukumomin tsaro gami da gami da nuna goyon baya tsakanin ma'aikatansu. Da yake kaddamar da gasar wasanni ta ma'aikatan tsaro (SESSA) a bana, Mills wanda Nii Nortey Dua, mukaddashin ministan harkokin matasa da wasanni na kasar Ghana ya karanta jawabi a madadinsa, ya ce gwamnati zata ci gaba da nuna goyon baya ga dukkan nau'o'in wasanni da nufin zakulowa kasar zaratan 'yan wasa maza da mata.
Ya kuma ce gasar zata samar da wata dama ta musamman ga 'yan wasa su nuna hazakarsu don su samu kasancewa cikin kungiyoyin kasa, su ciyo mata kyautuka a yayin gasannin kasa da kasa. Ya shawarci 'yan kasar ta Ghana da su dinga motsa jiki koda yaushe don zama cikin koshin lafiya, abin da zai tallafawa kasar cimma burin da ta kira " Sahihiyar ajandar Ghana".
A shekarar 1986 ne aka fara irin wannan gasar, inda hukumomin tsaro hudu suka kasance ciki. A halin yanzu, hukumomin tsaro shida ne ke halarta, wadanda suka hadar da, rundunar sojojin Ghana, rundunar 'yan sandan Ghana, hukumar kula da gidajen yari ta Ghana, hukumar kashe gobara ta Ghana, hukumar kula da harkokin shige da fice ta Ghana da hukumar hana fasa kwaurin kayayyaki ta Ghana. (Garba)