Kungiyar kwallon kafa ta maza ta kasar Ghana da aka ba ta lakabin Black Stars,wadda ke da niyyar cirar tutar gasar cin kofin Afirka a 2012,ta fara shekarar ne da zama na biyu a nahiyar Africa inda take biye da kasar Cote d'ivoire bayan da ta samu maki 18 a wannan shekara, wanda ya kara da na da ya zama maki 779.
Kasar Aljeriya ita ce na 3 sai kasar Masar na biye a matsayi na 4 a nahiyar baki daya kamar yadda mizanin awon ya nuna.
Zakarun duniya Kasar Spain har yanzu ita ke gaba a matsayi na daya a duniya sai kasar Netherland na biye da ita a matsayin na biyu sai na 3 kuma kasar Jamus.
Babbar hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA na sa ran samun wani canji a watan gobe na Fabrairu, ganin cewa za'a kaddamar da gasanni baki daya 32 a karkashin laimar babbar gasar cin kofin Afirka, wadda za ta fara a ranar 21 ga watan nan da muke ciki.
Kasar Ghana dai ta shiga karon kusa da na karshe a gasar cin kofin duniya da ta gudana a kasar Africa ta Kudu a shekara ta 2010.(Fatimah)