Baya ga haka bashin zai taimakawa kara tsawon wa'adin sakamakon gwajin farko biyu na tsarin da ya shafi masana'antun karkara da aka samu babbar nasara, wadanda cikin shekaru 16 da suka wuce suka samar da ayyuka masu kyau domin biyan bukatun jama'ar kauye ta hanyar ba da bashi mai riba ko samar da kayayyakin zamani domin bunkasa ayyukansu.
Tsarin kuma ya taimaka wajen bada horo kan sha'anin cigaban masana'antu da yadda ake tafiyar da aikin jagoranci da makamantansu. Asusun FIDA ta nuna cewa aikin noma kome kankantarsa wata masana'anta ce. Kokarin maida kananan ayyukan noma miliyan 500 zuwa wasu kananan masana'antu ya taimaka wajen raya aikin gona cikin dogon lokaci mai zuwa da samar da abinci ga jama'ar, tare da taimakawa bunkasuwar tattalin arziki.
A shekarar 2006, kasar Ghana ta kasance kasa ta farko a nahiyar Afrika da ta samu damar rage da rabin mutanen dake rayuwa cikin kangin talauci. Duk da wannan jimillar raguwar talauci a kasar Ghana, amma har yanzu yankunan karkara na cigaba da kasancewa cikin talauci musammun ma a arewacin kasar.
Tun daga shekarar 1980, asusun FIDA ya zuba kudade sau tari wajen gudanar da tsare tsare da ayyukan cigaban tattalin arziki da na al'umma guda 16 a kasar Ghana.(Maman Ada)