in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwamitin tsaron MDD ya yi kiran shawo kan abubuwa dake haifar da rikici a Afirka
2013-04-16 10:10:00 cri

A ranar Litinin ne kwamitin tsaro na MDD ya yi kiran a kara himma wajen shawo kan batutuwa dake haifar da rikici da nufin kawar da aukuwarsu, da ma tabbatar da gina zaman lafiya a nahiyar Afirka.

Kasar Ruwanda wacce ita ce ke kan mukamin shugabancin na karba-karba na kwamitin tsaron mai mambobi 15 a wannan wata, cikin wata sanarwa ta shugaba, ta bayyana cewa, an cimma wannan kuduri ne bayan muhawara kan hana aukuwar rikici a Afirka da ministan harkokin wajen kasar Ruwanda Louise Mushikiwabo ya jagoranta.

A cikin sanarwar, kwamitin tsaron ya jaddada cewa, aikin kwamitin shi ne ba da goyon baya ga kasashe mambobin MDD wajen hana aukuwar rikici da kuma tabbatar da muhimmancin hadin gwiwa.

Sanarwar har wa yau ta tabo muhimmancin kare yara a lokacin rikici, da ma irin rawa da mata za su taka a wajen gina zaman lafiya da kuma muhimmancin aikin kafa zaman lafiya na MDD.

A kuma ran Litinin din ne kasar Sin ta bayyana cewa, taimakawa Afirka ta cimma bunkasar tattalin arziki da zamantakewar jama'a abu ne muhimmi wajen shawo kan rikici a nahiyar, tare kuma da yin kiran hadin gwiwa da tafiyarwa na kasa da kasa.

Wakilin din din din na kasar Sin a MDD Li Baodong shi ne ya bayyana hakan yayin bude taro kan zaman lafiya da tsaro a Afirka mai taken "Hana aukuwar rikici a Afirka, gano abubuwa dake sababba rikici".

Li ya ci gaba da cewa, har yanzu a nahiyar Afirka ne aka fi samun rikici da tabarbarewar tsaro, inda ya jadadda cewa, daukar matakai masu inganci na da muhimmanci don kawar da aukuwar rikici a Afirka don tabbatar da zaman lafiya da tsaro a duniya baki daya.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China