A ranar Alhamis din nan ne babbar jami'ar MDD ta bayyana kalubalen tsaro da harkokin 'yan bindiga da ke ci gaba da kawo rashin daidaito a Sudan ta Kudu.
Wakiliyar musamman ta MDD a Sudan ta Kudu, Hilde Johnson ita ce ta bayyana hakan yayin da take jawabi ga kwamitin tsaro na MDD dangane da halin da ake ciki yanzu a sabuwar kasar ta duniya.
Jonglei wacce ita ce jiha mafi girma a gabashin kasar Sudan ta Kudu ta zamo fagen dagar yakin kabilanci tun lokacin da kasar ta nahiyar Afirka ta samu 'yanci, saboda 'yan kabilar Nuer da 'yan kabilar Murley, wadanda su ne kabilu mafi girma a jihar suna ta fada da juna dangane da rigingimu da suka shafi mallakar filaye da shanu.
A farkon shekarar nan, gwamnatin kasar ta yi wa jihar Jonglei lakabi da 'yankin bala'i' inda har ta tura sojoji guda dubu uku, don kokarin kawo karshen fada na kabilanci a jihar. Ita ma MDD ta tura dakarun guda dubu daya zuwa jihar.
A kuma yammacin Bahr el-Ghazal, akwai farar hula guda 5000 da suka yi gudun hijra zuwa sansanin hukumar MDD ta UNMISS a watan Disamban bara sakamakon fada tsakanin al'ummomi a Wau, in ji jami'ar.
Sakamakon haka, MDD ke kokarin aiki kut da kut da masu ruwa da tsaki don a samu goyon bayan fara sulhu.(Lami)