in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwamitin tsaro na MDD ya nuna damuwa kan yanayin tsaro a CAR
2013-03-21 10:09:36 cri

A ranar Laraba ne kwamitin tsaro na MDD ya nuna damuwa dangane da tabarbarewar tsaro a jamhuriyar Afrika ta Tsakiya (CAR) bayan da gammayar kungiyoyin adawa ta sanar da kawo karshen tsagaita bude wuta tsakaninta da gwamnati.

Wakiliyar musamman ta magatakardun MDD kan yanayi da ake ciki a CAR Margaret Vogt, ta yi bayani ga kwamitin tsaro na MDD mai mambobi goma sha biyar kan lamarin a sirri.

Sanarwa da aka bayar na nuni da cewa, kwamitin ya yi suka kan harin da 'yan tawayen gammaya ta Seleka suka kai a Bangassou da ma yankuna dake zagayenta, tare kuma da yin barazanar dawo da fadace fadace.

Col. Sylvain Bordas wanda shi ne mai magana da yawun 'yan tawayen gammayar Seleka ya yi bayani ran Litini a garin Bangui cewa, 'yan adawar ba za su yi wani jinkirin sake daukar makamai ba, muddin ba'a biya masu bukatunsu ba cikin sa'o'i 72.

Mambobin kwamitin tsaron sun nuna damuwa matuka dangane da yanayin da jama'a ke ciki, har ma da batun matsalar abinci, tare da yin kira ga dukkan bangarori da su dakatar da dukkan wani mataki na tayar da hankali da kuma cin zarafin farar hula, har da yara kanana.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China