in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugabannin sojojin kasashen Mauritania, Aljeriya, Mali da Nijar sun tattauna matsalar tsaro a Sahel
2013-03-28 12:30:30 cri

Kwamitin dake kunshe da shugabannin rundunar sojojin kasashen Mauritania, Aljeriya, Mali da Nijar ya yi wani zaman taronsa a ranar Laraba a Nouakchott, hedkwatar kasar Mauritania domin tattauna halin tsaro da ake ciki a yankin Sahel, a wani labarin da kamfanin dillancin labarai na Xinhua ya samu daga wata majiya mai tushe. Baya ga nazarin halin tsaro, shugabannin rundunar sojojin wadannan kasashe na yankin Sahel, da ke fama da barazanar ta'addanci, sun kuma mai da hankali kan hanyoyi da matakan da suka dace a dauka wajen kara karfafa dangantaka da kiyaye huldar dake tsakanin rundunonin wannan shiyya bisa la'akari da sabon kalubalen tsaron da ake fuskanta, a cewar wata sanarwar ofishin rundunar sojojin kasar Mauritania a gabanin wannan taro. Gamayyar wadannan kasashe ta kafa wata rundunar soja ta hadin gwiwa tun a shekarar 2011 wadda aka sake farfado da aikinta tun lokacin barkewar rikici domin fatattakar 'yan kishin Islama masu makamai dake arewacin kasar Mali. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China