Kwamitin tsaron mai mambobi 15 ya amince da kafa runduna ta musamman ta shiga tsakani a cikin hukumar kawo daidaito ta MDD dake aiki a jamhuriyar demokradiyar Congo (MONUSCO) na tsawon shekara daya, a matakin farko.
Bugu da kari, kwamitin tsaron ya jaddada muhimmancin tabbatar da zaman lafiya, tsaro da hadin gwiwa bisa yarjejeniya da aka kulla ran 23 ga watan Fabrairun shekarar 2013 dangane da tabbatar da zaman lafiya a gabashin kasar DRC, da ma yankin baki daya na tsawon lokaci.
Kwamitin ha rwa yau ya yi suka da kakkausar muraya dangane da ci gaban kasancewar 'yan tawayen kungiyar M23 a a cikin Goma da kuma yunkuri da suke yi na kafa gwamnati bi da bi ba bisa doka ba a yankin arewacin Kivu, in ji kudurin.
A ranar 5 ga watan Maris, magatakardan MDD Ban Ki-Moon ya yi kira ga kwamitin tsaro da ya ba da umurnin kafa rundunar shiga tsakani a DRC don shawo kan barazana ta zahiri ga zaman lafiya da tsaro.
Rikicin na DRC ya haifar da rashin muhallin jama'a da yawansu ya kai sama da dubu 475, kana sama da dubu 75 suna gudun hijira a kasashen Ruwanda da Uganda dake makwabtaka da kasar.(Lami)