in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Najeriya zai kai rangadi a arewa maso gabashin kasar dake fama da rashin tsaro
2013-03-07 10:46:30 cri

Shugaban tarayyar Najeriya Goodluck Jonathan zai kai wani rangadi a jihohin Borno da Yobe dake yankin arewa maso gabashin Najeriya masu fama da matsalar rashin tsaro.

Wannan rangadi ya zo bayan shekaru hudu da barkewar wannan rikici, a yayin kuma al'ummomin wurin suke fatan ganin hukumomin kasar sun kawo karshen wadannan tashe-tashen hankali dake da nasaba da 'yan kungiyar Boko Haram.

Shugaba Jonathan zai fara wannan rangadi na kwanaki biyu a ranar yau Alhamis a Maiduguri, hedkwatar Borno, haka kuma mazauna wannan yanki sun bayyana fatan ganin shugaba Jonathan ya gudunar da wannan ziyara cikin kwanciyar hankali da tsaro.

Muna fatan ganin shugaban kasa ya iso nan kuma ya koma ba tare da wani hadari ba, haka kuma wannan ziyara tasa ta taimaka wajen kawo karshen wannan rikici da ya jima da jihar take fama da shi tun cikin shekarun baya bayan nan, in ji mazaunan wannan jihar.

Yobe da Borno sun kasance sansanonin kungiyar Boko Haram da ta fara ta da borenta a shekarar 2009, tun wannan lokaci zuwa yanzu fiye da mutane 1500, ciki har mata da yara suka mutu sakamakon hare-haren wannan kungiya. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China