Manzon MDD da kungiyar tarayyar Larabawa ta AL don gane da rikicin kasar Syria Lakhdar Brahimi, ya yi kira ga dukkanin masu ruwa da tsaki don gane da rikicin kasar ta Syria, da su goyi bayan kiran da jagoran 'yan adawar Syria Moaz Al-Khatib ya yi, na komawa teburin shawarwari da mahukuntan kasar.
Brahimi ya yi wannan tsokaci ne yayin wani taron manema labaru na hadin gwiwa da babban sakataren kungiyar AL Nabil Al-Arabi, wanda ya gudana ranar Lahadi 17 ga wata a birnin Cairo na kasar Masar. A cewar Brahimi, kudirin komawa shawarwarin da Al-Khatib wanda a yanzu haka ke gudun hijira ya gabatar na nan daram, don haka ya jaddada bukatar da ake da ita ta rungumar shirin ba tare da wani bata lokaci ba.
Daga nan sai ya bukaci fara tattaunawa tsakanin bangarorin biyu a helkwatar MDD, matakin da Brahimi ke ganin shi ne zai bude kofar lalubo bakin zaren wannan matsala ta kasar Syria.
A nasa bangare, Nabil Al-Arabi cewa ya yi, ya shirya jagorantar wata tawagar kasashen Larabawa 4, wadanda za su gana da wakilan kasar Rasha a birnin Moscow, don gane da batutuwan da suka shafi bangarorin biyu, ciki hadda batun warware rikicin kasar ta Syria.
Ko da a farkon makon da ya gabata ma dai sai da Brahimi ya gana da Khatib, da kuma Al-Arabi, domin bayyana musu inda aka kwana ga batun ziyarar neman hadin kai da ya kai kasashe daban-daban, duka dai da nufin kawo karshen zub da jini a kasar ta Syria.(Saminu)