in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta yi tir da harin da aka kai a jami'ar dake arewacin Syria
2013-01-17 11:07:18 cri

Babban magatakardar MDD Ban Ki-Moon a ranar Laraba 17 ga wata da kakkausar murya ya yi tir da harin da aka kai a wata jami'a dake garin Aleppo na arewacin kasar Sirya, abin da bayani ya nuna ya halaka fiye da mutane 80, sannan ya jikkata 160, yana mai cewa, harin da aka yi da niyya a kan fararen hula wani babban laifi ne na yaki.

A lokacin taron manema labarai da aka saba yi a kullum, mataimakin kakakin magatakardar Eduardo del Buey ya ce, babban magatakardan ya nuna matukar bacin ransa.

Shi dai ababen fashewar da suka fashe har sau biyu sakamakon makami mai linzami da wasu masu dauke da makamai suka harba dab da jami'ar ya girgiza sashin koyon fasahar bayanan injiniya na jami'ar a ranar Talata 15 ga wata.

Aleppo, gari mafi girma ya zama babban matattarar tashin hankali tun da aka fara fada a kasar yau watanni 22, abin da Eduardo del Buey ya ce, ba za'a amince da shi ba, kuma ya zama wajibi ga dukkan bangarori da su kawo karshen shi nan take.

Ya kara da cewa, babban magatakardan ya mika ta'aziyarsa ga iyalan mamatan da kuma jaje ga wadanda suka raunata yana mai jaddada cewa, lallai ne wannan aika aika a tabbatar an yi bincike an gano wadanda suka aikata shi domin su fuskanci hukunci.

Mr. Ban Ki-Moon ya kuma yi kira ga daukacin al'umman kasar Syrya da su duba wannan al'amari da idon basira ganin yadda tashin hankali ke raba kasar su biyu, ya jaddada bukatar dake akwai na samar da zaman lafiya a siyasance wanda zai kawo karshen wannan fitina da ake fuskanta a kuma samar da demokradiyyar da al'ummar suke bukata.(Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China