in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sojojin Sham sun yi niyyar daukan matakai kan 'yan tawayen kasar
2012-12-24 10:15:14 cri

Rundunar sojin kasar Sham ta bayyana aniyarta ta cigaba da farautar dukkanin magoya bayan kungiyoyin tada kayar baya, dake burin ganin bayan zaman lafiya da tsaro a kasar. Wannan dai tsokaci da rundunar ta yi ranar Lahadi 23 ga wata ta kafar kamfanin dillancin labaran kasar SANA, ya zo daidai lokacin da 'yan adawar dake ikirarin mutuwar mutane da dama, sakamakon wani harin da suka kai tsakiyar yankunan kasar. Kamfanin dillancin labaran ya ruwaito rundunar sojin na bayyana irin nasarorin da ta samu kan 'yan tawayen a baya bayan nan, ciki hadda bankado, wani yunkuri na tashin bam a wani asibiti da ake kira al-Nahda, dake Daraya a wajen birnin Damascus, tare da gano wani kwarya kwaryar asibiti da 'yan adawar suka kafa a wata makaranta mai zaman kanta mai suna Ebaa al-Arabi, asibitin dake kunshe da kayayyakin kula da lafiya da magunguna da rundunar sojin ta ce, sato su aka yi daga wasu cibiyoyin gwamnati. A baya dai dakarun 'yan tawayen sun sha kai hare hare kan manyan cibiyoyi da turakun wutar lantarki, da bututun iskar gas, dama matakun danyan mai, da nufin gurgunta tasirin gwamnatin kasar, matakin da ya janyowa kasar ta Sham asarar miliyoyin daloli.

Ko da yake abu ne mawuyaci a iya tantance bayanan dake fitowa daga bangaren 'yan adawar, a hannu guda, wata kungiya mai rajin kare hakkin dan adam ta kasar Birtaniya, ta ce, mutane da dama sun rasu sakamakon wani harin da aka kai ta sama a garin Helfaya dake lardin Hama, baya ga dauki-ba-dadi da kungiyar ta ce, an yi tsakanin dakarun 'yan tawayen da sojojin gwamnati a wasu sassan kasar, al'amarin da ya sanya yawan wadanda suka rasa rayukansu a ranar ta Lahadi zarta mutane50.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China