Wata takardar bayan taro da suka sanya wa hannu bayan kammalar taron da suka gudanar a birnin Pelerin na kasar Switzerland, jami'an biyu sun bayyana takaicin yadda yunkurin warware wannan matsala ya ci tira a baya.
Daga nan sai suka nanata aniyar kasashen duniya, don gane da tsayawa tsayin daka, wajen kawo karshen wadannan kiki-kaka ta hanyar lumana, tare da kiyaye harkokin dukkanin al'ummar kasar.
Har ila yau, sakataren majalissar dinkin duniyan da Lakdar Birahimi, sun nuna rashin jin dadin su ga yadda a cewar su, tsagin gwamnatin Syria, dama na 'yan tawayen kasar ke dada watsi da batun martaba rayukan bil'adama a kasar, suna masu karfafa muhimmancin dake akwai, na baiwa batun hukunta laifukan yaki da cin zarafin bil'adama kulawa yadda ya dace. (Saminu Usman)