in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wani jami'in 'Red Cross' na ziyarar aiki a kasar Mali
2013-04-09 11:03:15 cri

Mataimakin darektan ayyukan agaji na kwamitin Red Cross, Regis Savios ya kai ziyarar aiki a ranar Lahadi a birnin Gao dake arewa maso gabashin kasar Mali, kuma ya samu ganawa a ranar Litinin tare da faraministan kasar Mali Diango Cissoko, a cewar wani labari daga hukumomin kasar.

'Na samu tattaunawa tare da faraminista game da matsalar jin kai a cikin kasar. Na kai ziyara a birnin Gao kuma wannan dalili ne da ya sa muka yi musanyar ra'ayi kan damuwar kwamitin Red Cross game da matsalar jin kai mai tsanani da ake fuskanta, ya zama wajibi mu canja ra'ayoyinmu bisa tsarin da za mu bi, ta yadda za'a tabbatar da hulda mai kyau tsakanin kasar Mali da kwamitin Red Cross,' in ji Regis Savioz da wata sanawar fadar faraministan kasar Mali ta rawaito kalamansa.

A cewar mataimakin darektan ayyukan kwamitin, matsala ta yi kamari sosai, har yanzu akwai wuya a gudanar da ayyuka a arewacin kasar Mali. Ko da yake a wasu yankunan ma'aikatanmu sun samu abinci ga iyalai fiye da dubu 420 a shekarar da ta gabata. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China