in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya da Amurka sun hada hannu kan yaki da ta'addanci
2013-03-06 10:18:45 cri

Hukumar ba da agajin gaggawa ta kasar Najeriya (NEMA) da cibiyar yaki da ta'addanci ta kasar Amurka sun fara wani shirin horo ga masu ruwa da tsaki kan tafiyar da yanayi idan aka fuskanci aukuwar wani bala'i.

Mai magana da yawun hukumar Yushau shuaib ya bayyana wa kamfanin dillancin labaran kasar Sin, Xinhua ta wata sanarwa da ya bayar ranar Talata a garin Abuja cewa, manufar shirin shi ne don a koyarwa ma'aikatan yadda za su ceto rayukan jama'a a yayin hari na ta'addanci.

Shirin horarwa da ake gabatarwa tare da hadin gwiwar cibiyar yaki da ta'addanci ta kasar Amurka, ya kunshi nuna yadda za'a yi amfani da na'urori wajen kare kai da kuma yadda za'a gwada yanayin guba ta hanyar amfani da na'urori.

Yayin bude shirin, darekta janar na hukumar NEMA Sani Sidi, ya ce, wannan shiri yana da muhimmanci ganin cewa, ana fuskantar harin 'yan ta'adda a Najeriya da yankin yammacin nahiyar Afirka.

Da yake magana, jakadan Amurka a Najeriya Terrence McCulley ya ce, shirin zai taimaka wajen gano kwarewa da kasar take da shi da kuma inda ta kasa har na irin bukatu da take da su a wannan fuska.

Ya ce, ba a Najeriya ne kadai ake fuskantar ta'addanci ba, domin ta zamo matsala a yankin yammacin Afirka baki daya, wato kamar a kasar Mali da ma wasu kasashen.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China