in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaba Obama na Amurka ya ba da tabbacin kulla kyakyawar hulda da Venezuela
2013-03-06 11:03:30 cri

Shugaban kasar Amurka Barack Obama ya ba da tabbaci ranar Talata cewa, a shirye kasar take ta kulla kyakyawar hulda da gwamnatin kasar Venezuela jim kadan bayan rasuwar shugaban kasar ta kudancin Amurka Hugo Chavez sakamakon cutar daji.

Cikin wata sanarwa daga fadar gwamnatin Amurka ta 'white house', shugaba obama na mai cewa, a wannan lokaci na kalubale bayan rasuwar shugaba Hugo Chavez, kasar Amurka na mai tabbatar da cikakken goyon bayanta ga jama'ar Venezuela da kuma burinta na kulla kyakyawar dangantaka da gwamnatin Venezuela.

Yayin da yake kiran wannan lokaci na karewar shugabancin Chavez wata sabuwar alkibla, shugaba Obama ya sha alwashin dagewa kan manufofi na dumokradiyya da kiyaye doka da kuma kare 'yancin bil adama a kasar dake kudancin Amurka.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China