Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayyana yau Talata cewa, kasar Sin a shirye take ta hada hannu da kasar Amurka a fuskar bunkasa hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu.
Xi ya bayyana hakan ne yayin wata ganawa da sakataren baitulmalin Amurka Jacob Lew, wanda zai kawo ziyara nan birnin Beijing ranar Talata da Laraba.
Shugaban ya yaba kyakyawan sakamako da dangantaka dake tsakanin kasashen biyu ta haifar, cikin shekaru talatin da suka gabata, inda jama'ar kasashen biyu suka amfana tare kuma da bunkasa zaman lafiya da daidaito a yankin Asiya-pasifik da ma duniya baki daya.
Lew ya taya Xi murna dangane da hayewa mukamin shugaban kasar Sin.
Ya yi kira ga bangarorin biyu da su bunkasa dangantaka a fannin tattalin arziki da muhimman batutuwa da kasashen biyu suke fuskanta da kuma tafi da banbanci dake tsakaninsu yadda ya kamata.(Lami)