in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin da Amurka sun fara zaman tattaunawa kan cinikayya na shekara shekara
2012-12-20 14:21:54 cri

A ran Laraba ne kasar Sin da Amurka suka fara tattaunawa a birnin Washington dangane da yaukaka huldar cinikayya da na kasuwanci tsakaninsu wanda suka saba yi shekara shekara.

Mataimakin firaminsita na kasar Sin Wang Qishan wanda a yanzu yake ziyara a Amurka shi ne ya jagoranci jiko na 23 na zaman tattaunawar tsakanin Sin da Amurka na hukumar hadin gwiwa ta kasuwanci da cinikayya JCCT tare da mukadashin sakataren kasuwanci na Amurka Rebecca Blank da wakilin Amurka a fuskar cinikayya Ron Kirk.

Da yake bayani yayin taron na JCCT jiko na 23 Wang ya ce, tattalin arzikin duniya na ci gaba da fuskantar manyan kalubale kuma masu wuyan gaske, kuma abu guda wanda shi ne kawai ya zamo tabbas shi ne cewa tafiyar hawainiya a fuskar farfado da tattalin arzikin duniya zai ci gaba da kasancewa a wannan yanayin da ake ciki.

Shi ma a nasa bayani yayin bude taron Kirk ya ce, taron na JCCT na daga cikin ginshikin dankon kawance tsakanin Amurka da kasar Sin.

Ita ma Blank ta ce, Amurka da kasar Sin su ne kasashe dake kan gaba cikin kasashe masu karfin tattalin arziki a duniya baki daya, kuma kawance dake tsakaninsu musamman ma a fuskar kasuwanci da cinikayya na da amfani matuka.

Blank ta yi kira ga kasashen biyu da su yi amfani da wannan dandali wajen cimma daidaito da kuma bunkasa harkar zuba jari da cinikkaya da ke kara samun ci gaba tsakaninsu.

An kafa wannan hukuma ta JCCT ne a shekarar 1983 don samar da dama ga kasar Sin da Amurka na yin tattaunawa kan muhimman batutuwa da suka shafe su da kuma bunkasa kawance a fuskar cinikayya.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China