in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Amurka ta tura wata tawagar kwararrun aikin soja zuwa Afrika
2013-01-18 10:29:13 cri

Kasar Amurka ta bayyana a ranar Alhamis cewa, za ta tura wasu masu horo a fannin aikin soja a wasu kasashen Afrika da suka shiga tura sojoji a kasar Mali domin fatattakar kungiyoyin kishin Islama.

'Muna son sanar da ku cewa, wasu rukunonin farko na tawagar ACOTA na kan hanyar zuwa Afrika, za su isa nahiyar nan da karshen mako domin fara ayyukansu', in ji kakakin gwamnatin kasar Amurka Victoria Nuland a yayin wani taron manema labarai, tare da bayyana cewa, wadannan tawagogi ba za su je Mali ba, sai dai a kasashen da za su tura sojoji domin horar da su.

Tsarin ba da tallafi da ba da horo kan ayyukan gaggawa a Afrika (ACOTA) na da burin horar da masu horo a fannin aikin soja da samar da kayayyaki ga rundunonin kasashen Afrika, ta yadda za su tafiyar da ayyukan tallafawa zaman lafiya da aikin jin kai.

Kasar Faransa ta shiga yaki a kasar Mali a makon da ya gabata, ta hanyar kai hare-hare ta jiragen sama kan sansanonin masu faffutuka, aikin da ya shiga gaban shirin tura sojojin kasashen Afrika da kwamitin tsaro na MDD ya amince a cikin wannan kasa dake yammancin Afrika.

Haka kuma kakakin White House, Jay Carney ya bayyana cewa, gwamnatin Amurka na cigaba da nazarin neman taimakon kasar Faransa domin Amurka da Faransa na da ra'ayi guda wato shi ne na hana 'yan kishin Islama da 'yan ta'adda su mai da kasar Mali ko wannan shiyya a matsayin wata cibiyarsu. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China