in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasashen duniya sun darajanta jawabin da shugaban kasar Sin ya bayar a dandalin Bo'ao na Asiya
2013-04-08 17:11:08 cri

A gun taron shekara-shekara na 2013 na dandalin nahiyar Asiya da aka bude a garin Bo'ao na kasar Sin a ran 7 ga wata, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya ba da jawabi, matsayin da ya dauka cikin jawabinsa na neman zaman lafiya, da samun bunkasuwa, da yin hadin gwiwa, da kawo moriyar juna a nahiyar Asiya da kuma duniya ya jawo hankali kuma ya samu yabo daga kasa da kasa, musamman ma daga kasashen Asiya da tekun Pasific.

Shugaban kamfanin dillancin labaru na kasar Indiya IANS Audday Basu, ya nuna cewa, jawabin Mr Xi ya jaddada manufar da Sin ke dauka na samun bunkasuwa cikin lumana, tare da bayyana cewa, Sin ba za ta gudanar da manufar kama-karya ba har abada.

Jaridar Lianhe Zaobao ta kasar Singapore ita ma ta ba da sharhi a shafin ta na Intanet, inda ta ce Xi Jinping ya jaddada matsayin da Sin ke dauka na sada zumunci da kasashen dake makwabtaka da ita, kana neman samun zaman lafiya, wani babban burin jama'ar kasar Sin ne. Ba kuma wanda zai iya kawo barazana ga yanayin duniya bisa san ransa.

A nata bangare jami'i mai kula da harkokin daidaita ayyukan kungiyar G20 ta kasar Rasha, kuma shugabar hukumar kididdigar kasar Ksenys Yudaeva cewa ta yi, dandalin Bo'ao zai taimakawa kasashe daban-daban, wajen sanin halin da tattalin arzikin da Sin, har ma da dukkanin duniya ke ciki, tare da fahimtar matsayin da Sin take dauka kan tattalin arzikin duniya. Ta ce, a halin da ake ciki na rashin samun tabbaci a fannin tattalin arziki, bunkasuwar tattalin arzikin kasar Sin cikin lumana, na da babbar ma'ana ga duniya baki daya.

Ban da wannan kuma kafofin yada labaru na kasashen Australiya da Kambodia da kasar Mongoliya da Korea ta Kudu su ma sun sa ido da jinjina sosai ga jawabin da Xi Jinping ya bayar. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China