in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bankin ECO ya yi alkawarin tallafawa masu zuba jarin kasar Sin
2013-04-10 14:16:40 cri

Mahukuntan bankin ECO na kasa da kasa, sun lashi takobin bunkasa harkokin kasuwancin masu zuba jari daga kasar Sin a yankunan Kudanci Sahara. A cewar shugabannin bankin, bude ofishin wakilci da suka yi a birnin Beijing na kasar Sin watanni 6 da suka gabata, wani mataki ne na habaka harkokin zuba jarin 'yan kasuwar kasar ta Sin a yankunan nahiyar Afirka

Shugaban bankin Thierry Tanoh, wanda ya amsa tambayoyin wakilin kamfanin dillancin labarum kasar Sin Xinhua, a ofishin kamfanin hada-hadar hannayen jarin kasar Ghana, bayan ya kammala takarar nasarorin da bankin ya cimma a shekarar bara, ya ce, kasar Sin, na kan gaba a fannin harkokin zuba jari a nahiyar Afirka. Don haka ya zama wajibi bankinsu, ya bunkasa yunkurin masu zuba jari daga kasar ta Sin a nahiyar Afirka.

Tanoh ya kara da cewa, bisa tagomashin da ofishinsu ya samu, tun lokacin da aka bude shi a birnin Beijing kawo yanzu, sun tabbatar da nasarar da za a iya samu daga cudanyarsu da 'yan kasuwa Sinawa.

Don gane da nasarorin da bankin na ECO ya cimma kuwa, jami'in ya ce, bankin wanda ke da rassa daban daban a kasashen Afirka 33, ya samu tsabar ribar da yawanta ya kai dalar Amurka miliyan 287 a shekarar ta bara, adadin da ya nuna karuwar ribar da kaso 39 bisa dari, idan an kwatanta da shekarun da suka gabata. Har ila yau, bankin na da kadarorin da kimarsu ta kai dala miliyan dubu 20, yayin da kuma kudaden ajiya suka tasamma dala miliyan dubu 15.

Bankin mai hedkwata a birnin Lome, na kasar Togo, na da rassa 1,200, da ofisoshin wakilci a Dubai da Landan da kuma birnin Beijing, yana kuma da ma'aikata 18,500, ya kuma samu kudaden masu zuba jari daga sassa kimanin 600,000.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China