Manazarta da dama na ganin cewa, batun fidda tsare-tsaren kafuwar bankin kungiyar manyan kasashe masu tasowa da ake wa lakabi da BRICS, zai taka muhimmiyar rawa a yayin taron kungiyar da za a yi a birnin Durban, daga ranar 26 zuwa 27 ga watan Maris mai kamawa.
Wani rahoto da wasu kwararru kan harkokin tattalin arziki Simon Freemantle, da Jeremy Stevens suka fitar, don gane da taron kungiyar ta BRICS karo na 5, wanda aka yi wa lakabi da "BRICS da Afirka, hadin kai domin bunkasa masana'antu", ya nuna cewa, akwai yiwuwar fidda gundarin tsarin kafuwar bankin da aka dade ana dakon gani.
Rahoton wanda kamfanin dillancin labarai na kasar Sin Xinhua ya samu kwafi, ya nuna cewa, makasudin kafuwar bankin shi ne, karkata akalar ci gaban kasashe mambobin kungiyar bisa tsarin bukatunsu, da kuma yanayin da ya dace da su. Don haka ake fatan bankin zai samar da tallafi ga ayyukan binciken inda aka sanya gaba, daga bisani kuma a fidda wata tawagar kwararru, da za ta samar da kyawawan manufofi da tsarin gudanarwar bankin.(Saminu)