in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gwamnonin babban bankunan kasashen Afrika sun bukaci wani tsarin kudi bai daya a nahiyar
2012-08-31 11:04:56 cri

Babban bankunan kasashen Afrika a jiya Alhamis 30 ga wata suka bukaci da a gaggauta kammala shirin shigar da amfani da wani tsarin bai daya na amfani da kudi a nahiyar a wani matsayi na samun nasarar aiwatar da dalilin kafa babban bankin Afrika wanda shi ne a iya fitar da kudin bai daya da kasashe za su iya amfani da shi.

Wakilai daga kasashe 31 na babban bankunan da kuma wassu bankuna daga nahiyar Afrika da hukumomi masu zaman kansu sun hadu a taro na 36 na kungiyar gwamnonin babban bankunan kasashen su a garin Algiers, babban birnin kasar Algeriya.

A lokacin taron, 'yan kungiyar sun zabi gwamnan babban bankin kasar Algeriya Mohammed Laksaci a matsayin sabon shugaba wanda ya maye gurbin tsohon shugaban Charles Chuka gwamnan babban bankin kasar Malawi da ya kammala wa'adinsa na shekaru 4.

Bayan zaben, Laksaci ya sheda ma manema labarai cewa, zai maida hankali ne a kan kafa wani hadin gwiwa tsakanin babban bankunan kasashen Afrika da kuma kasashen nahiyar ta Afrika.(Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China