Kudin ajiyar babban bankin kasar Mauritania BCM ya cimma wani sabon matsayi a shekarar 2012, a cewar wani rahoton cibiyar bincike ta kasa da kasa ta 'Ernest and Young' da kafofin kasar Mauritania suka rawaito a ranar Lahadi.
Jimillar ribar ajiyar kudin musanya na babban bankin BCM da aka kiyasta a ranar 31 ga watan Disamban shekarar 2012 ya kai dala biliyan 978.5, in ji wannan rahoton da kamfanin dillancin labarai AMI na kasar Mauritania ya rawaito.
Wannan shi ne, a cewar AMI, wani rahoton karshe na cibiyar kasa da kasa ta 'Ernest and Young' bisa amincewar kudaden ajiyar kasa da kasa da na kudaden da ake samu cikin gida zuwa 31 ga watan Disamban shekarar 2012.
Wannan hali ya bayyana karfin dabarun tattalin arziki da kudi da ake gudanar da kuma ingancin manufar kudin musanya, a cewar kwararru a wannan fanni.
Manufar kudi ta bankin BCM ta samu tsokaci sosai a bangaren 'yan adawa, wadanda suke kimanta wannan hukuma a matsayin wani makamin dake hannu masu iko maimakon wani makamin daidaita tsarin harkokin banki. (Maman Ada)