in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Halin da ake ciki a kasar Syria na kara tabarbarewa, in ji wakilin MDD
2012-11-30 10:13:30 cri

Wakilin musamman na MDD da kungiyar tarayyar kasashen Larabawa kan kasar Sham Lakhdar Brahimi ya ce, halin da ake ciki a kasar ta Syria sai kara tabarbarewa yake yi.

Da yake zantawa da 'yan jarida, Brahimi ya yi hasashen cewar, zai jadadda wannan batu yau Juma'a, a jawabin da zai gabatar ga babban taron MDD a kan Syria.

Ya ce, "Masu rikicin kansu ba su da niyyar samo hanyar warware rikicinsu, kuma yankin kansa ba shi da wani tasirin taimakawa a samo hanyar sassantawa cikin lumana. Saboda haka, majalisar tsaron MDD ce kadai za ta iya yunkurin yin sulhu."

Mataimakain mai magana da yawun MDD Eduardo Del Buey ya bayyana cewa, magatakardan MDD Ban Ki-Moon ya yi wata ganawa da Brahimi ran Laraba da safe, inda sakatare janar din ya sha nanata cewa, babu wata dabarar amfani da karfin soja da za ta kai ga cimma shawo kan rikicin a Syria.

Brahimi ya ce, "Kalubalen da aka dora shi ne na bullo da wata dabara, kuma yanzu haka mun fara tsara wannan dabara, to amma tsarin namu ba zai samu kammalawa ba sai majalisar ta zauna ta duba, ta kuma cimma kudurin yin shimfidar warware rikicin ta hanyar siyasa."(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China