Kamfanin dillancin labarai na kasar Sin Xinhua ya samo mana labarin cewa, shugaban kasar Sudan Omar El-Bashir a ranar Talata 12 ga wata ya amsa goron gayyatar takwaransa na kasar Sudan ta kudu Salva Kiir Mayardit domin ziyartar Juba babban birnin kasar.
Kamar dai yadda kamfanin dillancin labarai na kasar Sudan SUNA ta sanar, an ce, shugaba El-Bashir ya amsa goron gayyatar ta ziyartar Sudan ta kudu, sai dai bai fadi ranar da zai yi wannan ziyarar ba.
A cewar mai ba da shawara ga shugaba El-Bashir ta fannin yada labarai Imad Sid Ahmed, shugabannin biyu a ranar Talata suka tattauna ta wayar tarho, inda suka taya juna murna game da rattaba hannu a kan yarjejeniyar inganta tsaro tare da amince wa da abin da suka yi da cewa, abu ne da ke wakiltan zamantakewar lumana na kasashen biyu, kuma a lokacin zantawarsu, El-Bashir ya jaddada muhimmancin dage wa na ganin an cimma abin da aka tattauna a kai.
Haka kuma shugabannin biyu sun tabbatar da bukatarsu duka na ganin sun karfafa dangantaka a tsakanin kasashen nasu.
Khartoum da Juba dai a ranar Lahadin da ta gabata suka fara janye sojojinsu daga kan iyakokin hadin gwiwa gabannin samar da kan iyaka mara sojoji domin share fagen rattaba hannu kan yarjejeniyar da aka sanya ma hannu.(Fatimah)