in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Nijar da Turkiya sun bullo da dokokin karfafa cigaba da bunkasa huldarsu
2013-01-10 10:14:18 cri

Kasashen Nijar da Turkiya sun cimma matsaya tare da sanya hannu a kwanan nan a birnin Yamai kan wasu yarjejeniyoyin kafa hanyoyin shari'a domin karfafa da cigaba da bunkasa dangantaka a tsakaninsu, a cewar wata sanarwar hadin gwiwa da ta biyo bayan karshen ziyarar aiki ta kwanaki biyu da faraministan kasar Turkiya, mista Recep Tayyip Erdogan ya kai kwanan nan a kasar ta Nijar.

Shugaban gwamnatin kasar Turkiya ya je kasar Nijar tare da wata babbar tawaga da ta hada musammun ma da manyan jami'an gwamnati, 'yan kasuwa da kuma masu zuba jari. Mista Erdogan ya samu ganawa da shugaban kasar Nijar Mahamadou Issoufou, da kuma yin shawarwari tare da sauran manyan jami'an kasar Nijar, kafin ya halarci wani zaman taro da ya tattara wakilan tawagogin kasashen biyu.

Domin cimma damar kafa dokokin karfafa da bunkasa hanyoyin huldarsu, kasashen biyu sun rattaba hannu kan wasu yarjejeniyoyin da suka shafi huldar tattalin arziki, kasuwanci da fasaha, da wasu yarjejeniyoyin da suka shafi fannin ruwa, samar da ruwa masu tsabata da tsabtace muhalli.

A wani labari na daban, gwamnatin Nijar ta nuna maraba da bude hanyar jirgin sama tsakanin kasar Turkiya da Nijar da kamfanin jiragen saman Turkish Airlines ya yi, kamar yarjejeniyar sufurin jiragen sama ta tanada da kasashen biyu suka sanya wa hannu a birnin Ankara a ranar 31 ga watan Mayun shekarar 2012 da kuma yarjejeniyar fahimtar juna dake ba da damar bude hanyar jiragen sama. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China