A gun taron manema labaru da aka shirya a wannan rana, Moussa Sinko Coulibaly ya bayyana cewa, za a kada kuri'a a zagaye na farko domin zaben shugaban kasa a ranar 7 ga watan Yuli na bana, sannan za a kada kuri'a a zagaye na biyu da kuma gudanar da zaben 'yan majalisu a ran 21 ga watan Yuli mai zuwa.
Bisa kundin tsarin mulkin kasar Mali, lashe zaben ya danganta ne da samun kuri'u sama da kashi 50 cikin dari ga dan takara. In ba haka ba, 'yan takara guda biyu da suke kan gaba wajen yawan samun kuri'u, za su shiga zagaye na biyu.
A ran 21 ga watan Maris na bara, wasu sojojin kasar Mali sun hambarar da mulkin Toure, suka kuma kafa kwamitin farfado da diplomasiyya da sake kafa kasar Mali, domin gudanar da ayyukan gwamnatin kasar.
A watan Afrilu na bara, kwamitin ya amince da mika mulkinsa ga shugaban majalisar dokokin kasar a lokacin, Dioncounda Traoré.
Sakamakon juyin mulkin soja, kungiya mai tsattsauran ra'ayi da 'yan ta'adda sun mamaye wasu yankunan dake arewacin kasar Mali, a kuma ran 20 ga watan Disamba na bara, kwamitin sulhu na MDD ya ba da izni ga kungiyar ECOWAS da ta tura tawagar tallafi dake karkashin jagorancin kasashen Afirka zuwa Mali, a kokarin taimakawa kasar wajen kwace wadannan yankuna daga hannun dakarun.
A ran 11 ga watan Janairu na bana, bisa bukatar gwamnatin kasar Mali, Faransa ta dauki matakan soja kan dakaru masu adawa da gwamnatin kasar Mali. A kwanan baya, shugaban rikon kwarya na kasar, Dioncounda Traoré ya furta cewa, za a gudanar da babban zaben kasar a watan Yuli na bana.(Fatima)