Mataimakin babban sakataren MDD mai kula da harkokin siyasa, Taye-Brook Zerihoun, ya shaidawa kwamitin mai mambobin kasashe 15 cewa, "ana bukatar canji a kokarin da MDD ke yi a wannan lokaci na shirin mika mulki da samar da zaman lafiya a Somalia".
Zerihoun ya ce, ya goyi bayan shawarar da babban sakataren MDD Ban Ki-moon ya bayar a rahotonsa na baya-bayan nan game da samar da tawagar wanzar da zaman lafiya a Mogadishu, babban birnin kasar Somalia, ta yadda za a samar da goyon baya ga shirin wanzar da zaman lafiya tare da hanzarta cimma nasarar manufofin jin kai.
Ya ce sabon shirin zai kunshi ofisoshi masu kyau, shawarwari da taimakawa kan tsaro, wanzar da zaman lafiya da gina kasa, shirya zabe, kare hakkin bin-adama da bin doka tare da tallafawa wajen gudanar da tallafin kasa da kasa.
Ita dai wannan shawara, ta biyo bayan tattaunawa da aka yi game da yadda aka kimanta dabarun da aka gudanar ne a karshen shekarar da ta gabata, da hukumomin Somalia, AU, kungiyoyin fararen hula da abokan huldar kasa da kasa da ke Somalia da Kenya.
Jami'in ya ce, hukumomin MDD da ke aiki a Somalia, sun hada da ofishin kula da harkokin siyasa na MDD(UNPOS) da UNSOA wanda ke samar da kayayyakin aiki ga dakarun AU da ke aikin wanzar da zaman lafiya a Somalia(AMISON), kuma ana shirin canja musu matsuguni zuwa Somalia na tsawon wa'adin sama da watanni 6-12.(Ibrahim)