Shugaba Hollande ya bayyana cewa, sojojin kasar Chadi ne suka kai hari ga dakarun 'yan tawaye dake yankin Ifolas a ranar 22 ga wata, wanda ya haddasa mutuwa da raunatar sojojin bangarorin biyu da dama. Ya ce, dakaru masu tsattsauran ra'ayin na boye a wannan yanki, don haka za a ci gaba da kai hare-hare a yankin. Wannan dai shi ne matakin karshe na yakin da sojojin kasar Faransan suke yi a kasar ta Mali.
A nata bangare rundunar sojan kasar Chadi ta tabbatar da cewa, a ranar 22 ga wata, sojojinta 13 sun mutu a sakamakon musayar wuta da ta auka a tsakaninsu da dakarun 'yan tawayen kasar ta Mali, kuma an harbe dakarun 65, wadanda ke da nasaba da kungiyar al-Qeada har lahira. Bisa labarin da aka bayar, an ce, yawan sojojin da suka mutu a wannan karo ya haura na sojojin kasar Faransa da kasashen Afirka da suka ba su a baya, sanaddiyar wannan yaki. (Zainab)