Shuagaban rikon kwarya na kasar Mali Dioncounda Traore ya fada a ranar Larabar nan 13 ga wata cewa, yakin da ake yi da masu tsattsauran ra'ayin addini a arewacin kasar ya dauki sabon salo, inda 'yan kungiyar ke amfanin da harin kunar bakin wake, sai dai wannan wani salo ne da aka san cewa za'a iya fuskanta.
Shugaban ya fadi hakan ne a Bamako babban birnin kasar a wajen rantsar da tsohon jagoran juyin mulkin da aka yi a kasar Ahmadou Haya Sanogo a matsayin shugaban kwamitin tsaro na sojoji da ke da alhakin yin kwaskwarima a rundunar tsaron kasar.
Ya ce, " mun san da cewa, muddin muka fara aiwatar da wannan fito na fito da su za mu fuskanci harin kunar bakin wake, wannan wata dabara ce da 'yan tawaye ke amfani da ita. Sai dai mun san iyakacin inda za su iya kaiwa ke nan, don haka muna bada tabbacin cewa, za mu kore su a yankin kasarmu".(Fatimah Jibril)