Bisa sanarwar da kungiyar EU ta bayar, an ce, wani ayarin share fage na tawagar horar da sojoji ya riga ya isa birnin Bamako hedkwatar kasar Mali a ranar 12 ga wata, kuma za a jibge dukkanin jami'an tawagar kafin karshen watan Maris.
Sanarwar ta bayyana cewa, a karkashin inuwar kuduri mai lamba 2085 na kwamitin sulhu na M.D.D., kungiyar EU za ta tura rundunar horar da sojoji zuwa Mali, kuma wannan zai zama wani matakin da za a dauka don kulawa da yanayin da ake ciki a kasar, da ma yankunan da ke hamadar Sahara.
Bisa labarin da aka bayar, an ce, rundunar horar da sojoji a Mali da kungiyar EU ta tura, za ta gudanar da aikin horar da sojoji, da ba da guzuri, da kuma koyar da su ayyukan jagoranci da dai sauransu. Ban da wannan kuma, tawagar horar da sojoji za ta ba da shawarwari ga sojojin gwamnatin Mali game da ka'idojin aikin jin kai na duniya, da kare rayuwar jama'a, da kiyaye hakkin dan Adam. Bugu da kari, bisa wannan kuduri, rundunar horar da sojojin ba za ta shiga cikin yaki kai tsaye ba.(Bako)