in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasashen duniya na sa kaimi ga warware rikicin Mali ta hanyar siyasa
2013-02-18 16:40:00 cri
Jaridar Peaple's Daily ta kasar Sin ta buga wani bayani a ran 17 ga wata cewa, yadda sojin hadin kai na kasar Faransa da Mali za su tabbatar da ikon yankuna da suka maido da su, da kuma yadda tawaga ta musamman ta kasa da kasa dake karkashin jagorancin kasashen Afrika da sauran rundunar sojin daga kasashen Afirka za su karbi aiki daga hannun sojin Farasna sun zamo muhimmin abubuwan da suka jawo hankulan bangarori daban-daban.

Kungiyar gammayar kasashen yankin Sahel–Sahara ta yi kira a ran 16 ga wata a gun wani taron koli da aka yi a birnin Ndjamena, hedkwatar kasar Chadi cewa, ya kamata, mambobin kasashen kungiyar su yi hadin gwiwa domin goyon bayan matakin soja da Mali ke dauka da yunkurin warware rikicin kasar ta hanyar siyasa, da kuma tinkarar 'yan ta'adda wadanda suke kawo babbar illa ga zaman lafiya a wannan yanki.

Bayanin kuma ya yi nuni da cewa, kafa wata gwamnati mai karfi da za ta samu amincewa daga bangarori daban-daban ya zama abin bukata ne na gaggawa a yau.

A halin yanzu, kasashen duniya na kara kokarin ba da gudummawa ga kasar Mali.

Bayanin ya dauka cewa, da akwai wahaloli da yawa wajen yunkurin warware rikicin kasar Mali ta hanyar siyasa.(Amina)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China