05-Apr-2026
04-Apr-2026
03-Apr-2026
02-Apr-2026
01-Apr-2026
20260405-Yamai
00:00
1x
Yanzu haka ana shirya karin gasannin wasan kwallo kafa, a matakin ‘yan wasa marasa kwarewa a sassa daban daban na kasar Sin, gasannin dake mayar da ‘yan wasan kwallo marasa kwarewa masu matukar farin jini a garuruwansu, tare da mayar da gasannin kwallon da ake bugawa a karshen mako wasu irin bukukuwa masu kayatarwa.
30-Mar-2026
28-Mar-2026
Ko da yaushe kasar Sin na mayar da hankali sosai kan ba da tabbaci ga tsofaffi a kauyuka wajen samun kulawa, da shigar da mata cikin harkokin siyasa na kasar. A yayin manyan taruka biyu na shekarar 2026 da aka rufe ba da dadewa ba, wato taron majalisar wakilan jama’ar kasar da na majalisar ba da shawarwari han harkokin siyasa ta jama’ar kasar, an ci gaba da mayar da hankali kan batun kula da tsofaffi a kauyuka a matsayinsa na muhimmin aiki na zaman rayuwar al’umma. Wasu ’yan majalisar wakilai mata da dama, wadanda suka fito daga kananan hukumomi, bayan gudanar da bincike mai zurfi da suka yi a karkara, bisa ga irin tausayi da himmar da mata suka kebanta da su, sun yi kira da a taimaka wa tsofaffin mazauna karkara wajen magance matsalolin da suke fuskanta na samun kulawa yadda ya kamata, wannan kuwa ya nuna irin fatan da manoma miliyoyi ke da shi na samun tabbaci a fannin.