Yanzu arewacin duniyarmu ta shiga lokacin zafi, inda mutane da yawa su kan ajiye abincin da ya rage a cikin firiji ko kuma firiji, na'urar sanyaya abinci, saboda suna tsammanin cewa, ajiye abinci a cikin firiji yana iya tabbatar da danyen abinci da kuma rage zafin abincin. Amma duk da haka, firiji, ba sef din da aka iya ajiye abinci a ciki ba ne. Wasu kwayoyin cuta wadanda suka saba da yanayin sanyi, suna boyewa cikin abincin da aka ajiye cikin firiji, ciki had da kwayar cutar Listeria Monocytogenes mafi hadari. An yi kashedin da cewa, abincin da ba a iya dumama su cikin sauki ba, da madara, kayayyakin madara, kayayyakin lambu da abincin ruwa, abinci ne da suka fi fuskantar barazanar kamuwa da kwayar cutar ta Listeria Monocytogenes.
An ruwaito cewa, kwayar cutar Listeria Monocytogenes, wani nau'in kwayar cuta ce wadda ke haddasa cututtukan da dabbobi ke yadawa Bil Adama. Ana iya samun ta a wurare da yawa a duniyarmu. Kwayar cutar na da suna na daban, wato mai kisan kai a cikin firiji. Tana iya ci gaba da rayuwa tsakanin digiri Celsius sifiri da kuma digiri Celsius 45, musamman ma a cikin firiji, tana iya rayuwa da kuma haihuwa. Kwayar cutar Listeria Monocytogenes da ke cikin abinci tana kawo wa tsaron lafiyar al'umma barazana. Idan ta harbi mutane, mutane kan yi zazzabi, da ciwon kai. Idan ba a gano kwayar cutar Listeria Monocytogenes ce ta haddasa ciwon kan lokaci ba, kuma ba a ba su jinya cikin hanzari ba, to, ciwon sankarau zai kama mutanen, ko kuma sauran kwayar cutar za ta shiga dukkan sassan jikin mutanen.
Madam Zhang Chuji, wata likita ce da ke aiki a asibitin Tiantan na Beijing, ta ba da shawarar cewa, kada a dade ana adana abinci cikin firiji. Haka kuma kada a ci abincin da ya rage kuma a ajiye shi cikin firiji, tare da dumama shi yadda ya kamata. Daukar mintoci 5 zuwa 20 wajen dumama abincin zuwa digiri Celsius 60 zuwa digiri Celsius 70 yana iya kashe kwayar cutar baki daya. Sa'an nan kuma, tsoffafi, kananan yara, masu juna biyu, wadanda suka dade suna fama da wasu cututtuka da sauran mutanen da ba su da garkuwa sosai, ya kamata su rage cin danyen abincin da ba a dafa ba, su rage shan abubuwan sanyi, a kokarin rage barazanar da suke fuskanta wajen kamuwa da kwayar cutar Listeria Monocytogenes. Ban da wannan kuma, ya zama dole a tsabtace firiji a kai a kai, don magance shi daga zama gidan kwayar cutar Listeria Monocytogenes. (Tasallah Yuan)