A baya a idon mutane, kananan yara kan nitse cikin ruwa mai zurfi har su mutu, amma Madam Zhang Chuji, wata likita da ke aiki a asibitin Tiantan na Beijing ta yi mana karin bayani da cewa, jarirai ba su iya kare kansu da kyau, shi ya sa idan bakinsu da hancinsu sun nitse cikin ruwan da zurfinsa ya kai milimita 2, cikin mintoci 2 su kan mutu sakamakon kwarewa.
Madam Zhang Chuji ta kara da cewa, gazawa wajen kulawa da kananan yara, shi ne daya daga cikin muhimman dalilan da suke haddasa mutuwar kananan yara sakamakon nitsewa cikin ruwa. Duk da haka kananan yara kamata ya yi su magance nitsewa cikin ruwa. Kada su kambama fasaharsu ta ninkaya. Ya zama tilas su yi ninkaya a wuraren da ke akwai ma'aikatan ceto masu lasisi. Kada su yi iyo a wuraren masu hadari ko wuraren da ba su sani sosai ba. Kada kananan yara su yi abubuwa masu hadari a cikin ruwa. Ban da haka kuma, kada su yi ninkaya yayin da suke jin yunwa, ko bayan da suka ci suka koshi, ko sun gaji, ko yin barci, ko sun ji ciwo. Ya zama dole su yi ninkaya yayin da suke cikin koshin lafiya.
Ko yin ninkaya a dakin ninkaya yana iya kare kananan yara daga mutuwa sakamakon nitsewa cikin ruwa? A'a, ba haka ba ne! Ko da ana ninkaya cikin dakin ninkaya, wajibi ne iyaye su raka 'ya'yansu ko kuma kananan yara su yi iyo tare. Haka zalika dole ne a tabbatar da ma'aikatan ceto suna iya kallon kananan yaran. Kafin a fara yin iyo, wajibi ne a motsa jiki da kyau. Idan kananan yara ba su motsa jiki kafin su yi tsalle cikin ruwa ba, to, ruwan mai sanyi kan haifar da ciwo sakamakon murdewar gwanji, ta haka yaran su yi saukin nitsuwa cikin ruwan, har su rasa rayukansu.
Idan an gano wani ya nitse cikin ruwa, to, kada kananan yara su je neman cetonsa da kansu. Ya kamata su yi ihu don kirawo mutane, haka kuma su nemi kayayyaki, su jefa su ga wadanda suke cikin ruwan, ta haka za su dogara da kayayyakin don kasancewa a kan ruwa. Ban da haka kuma, kada a kubutar da mutane fuska da fuska cikin ruwa! Saboda mai yiwuwa ne wadanda suke cikin ruwan za su ji matukar tsoro, za su kama wadanda suke kokarin cetonsu sosai, ta yadda dukkansu ba za su iya fitowa daga ruwa ba, a karshe dai za su mutu duka.
Madam Zhang ta kuma yi karin bayani da cewa, bai kamata a danna kirjin wanda ya shide don kokarin dawo da numfashin sa a cikin ruwa ba, kana kuma bayan da aka kubutar da kanana yara daga cikin ruwa, kada a goya su a baya ta hanyar rike kafafun su, kan su kuma a kasa don ruwan da ke cikin jikinsu ya fita waje, hakan ya bata lokacin ba su jinyar gaggawa. Ya zama tilas da zarar an kubutar da kananan yara daga ruwa, sai a hanzartar danna kirjin wanda ya shide don kokarin dawo da numfashin sa, har ila yau kada a danna kirjinsu kawai, a manta da hura musu numfashi. (Tasallah Yuan)