in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
'Yan kasa da shekaru 20 suna rabin saukin kamuwa da COVID-19 kan wadanda ke da shekaru 20 ko fiye da haka
2020-07-13 08:35:58 cri

Wani sabon rahoton nazari da aka kaddamar a kwanan baya dangane da ilmin yaduwar cututtuka a mujallar kimiya ta Nature Medicine ya nuna cewa, 'yan kasa da shekaru 20 suna da rabin saukin kamuwa da annobar cutar numfashi ta COVID-19 na wadanda ke da shekaru 20 ko fiye da haka. Rahoton ya kuma kimanta cewa, kashi 21 cikin dari ne kawai daga cikin wadanda shekarunsu suka wuce 10 amma ba su kai 20 a duniya ba su kan nuna alamun kamuwa da cutar, adadin da ya karu zuwa kashi 69 cikin kashi dari a cikin wadanda ke da shekaru 70 ko fiye da haka.

Wannan rahoton nazari ya yi nuni da cewa, kara sanin muhimmancin shekarun mutane na haihuwa a fannonin yaduwar annobar ta COVID-19 da kuma yadda suke fama da ita, yana da matukar muhimmanci wajen kimanta amfanin ba da tazara yayin mu'amala da juna da kuma yin hasashen yawan masu kamuwa da annobar a duk fadin duniya. Ya zuwa yanzu dai yawan kananan yara da suka harbu da annobar ta COVID-19 a duniya baki daya ba shi da yawa sam. Kila dalilan da suka sa haka su ne domin kananan yara ba su da saukin kamuwa da cutar, kana ba safai su kan nuna alamun kamuwa da cutar ba.

Masu nazari daga kwalejin ilmin likitanci a yankuna masu zafi na London da ke kasar Birtaniya sun tantance bayanan da suka shafi al'ummomi daga yankuna 32 na kasashen Sin, Italiya, Japan, Singapore, Canada da Koriya ta Kudu da kuma alkaluma guda 6 masu ruwa da tsaki. Sun kuma fito da wata dabarar yin hasashe bisa shekarun mutane na haihuwa, kan shin wani ko wata ta/yana da saukin kamuwa da cutar ko a'a, da kuma shin zai ko za ta nuna alamun kamuwa da cutar ko a'a. Masu nazarin sun gano cewa, a duk wadannan yankuna 32, 'yan kasa da shekaru 20 suna rabin saukin kamuwa da COVID-19 kan wadanda ke da shekaru 20 ko fiye da haka. A cikin wadanda shekarunsu suka wuce 10 amma ba su kai 20 a duniya ba, kashi 21 cikin dari ne kawai suka nuna alamun kamuwa da cutar, yayin da adadin ya kai kashi 69 cikin kashi dari cikin wadanda ke da shekaru 70 ko fiye da haka.

Masu nazarin sun kuma yi nazari kan yadda annobar ta COVID-19 take yaduwa a manyan birane 146 a duniya. Inda suka gano cewa, a daidai lokacin da ba a samun sassaucin yaduwar annobar, yawan masu kamuwa da cutar a cikin wadannan birane sun sha bamban sosai bisa shekarun mutane a wurin. Idan akwai tsoffafi da yawa a wurin, to, masu kamuwa da cutar wadanda suka nuna alamun kamuwa da cutar sun fi yawa a wurin. Amma idan akwai matasa da yawa a wurin, wadanda ba sa nuna alamun cutar sun fi yawa.

Masu nazarin sun yi bayani da cewa, za su ci gaba da nazarinsu don tabbatar da ko wadanda ba sa nuna alamun cutar za su iya yada annobar ga wasu ko a'a, ta haka za a yi hasashen yaduwar annobar yadda ya kamata. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China