Madam Zhang Chuji, wata likita ce da ke aiki a asibitin Tiantan na Beijing ta yi mana karin bayani kan amfanin maganin statins, inda ta ce, ana amfani da maganin na statins wajen rage yawan maikon da ke cikin jikin dan Adam, da rage aikin kwayoyin garkuwar jiki, da rage kumburi da kuma rage barnar da cutar ke yi ga huhu. Kullum masu fama da cutar ta COVID-19 mai tsanani su kan fuskanci matsalolin da muka ambata a baya, wadanda kuma su kan yi barna kan sassan jikin masu fama da cutar.
Wannan sabon nazari da aka gudanar kan amfanin maganin statins ta fuskar yaki da cutar ta COVID-19 ya tantance yadda masu fama da cutar 13,981 suke shan maganin. An gano cewa, yawan mutuwar masu fama da cutar wadanda suka sha maganin na statins ya ragu da kaso 45 cikin dari.
Ban da haka kuma, nazarin ya nuna cewa, shan maganin statins tare da sauran magungunan tabbatar da daidaita hawan jini ba zai kara yawan mutuwa ba.
Masu nazarin sun yi bayani da cewa, sakamakon nazarinsu ya kasance wani shaida dake tabbatar da ingancin maganin statins wajen warkar da masu fama da cutar COVID-19 da suka samu jinya a asibiti da kuma kyakkyawar kariyar da maganin yake ba su. Haka zalika an karfafa gwiwar masu nazari da su ci gaba da nazarinsu kan amfanin maganin statins wajen shawo kan cutar ta COVID-19.
Amma duk da haka, masu nazarin sun nuna cewa, ko da yake alkaluman sun kasance shaida dake tabbatar da ingancin maganin statins, amma akwai bukatar ci gaba da nazarin kan karin mutane.
Ya zuwa yanzu dai ba a samu allurar rigakafin cutar COVID-19 ko kuma sabuwar hanyar shawo kan cutar ba tukuna. Amma maganin statins da kuma maganin Remdesivir suna taimakawa wajen shawo kan cutar.
Maganin statins, wani nau'in magani ne da a kan yi amfani da shi a duk fadin duniya. A kasar Birtaniya mutane fiye da miliyan 7 ne suke shan maganin a ko wace shekara.
Ko da yake maganin statins yana taimakawa wajen shawo kan cutar ta COVID-19, amma ya zama tilas a bi shawarar likitoci kafin a sha maganin. (Tasallah Yuan)