in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ta yaya za mu kiyaye kanmu daga tsananin zafi da kuma annobar cutar numfashi ta COVID-19?
2020-08-04 10:47:51 cri

Ya zuwa yanzu annobar cutar numfashi ta COVID-19 tana yaduwa a wasu kasashe, haka kuma duniyarmu ta arewa ta shiga lokacin zafi, inda tsananin zafi kan sanya mutane su kara fuskantar barazana. To, ta yaya za mu kare kanmu daga tsananin zafi da kuma annobar? Kwararru daga hukumar kiwon lafiya ta kasa da kasa da kuma hukumar yanayi ta kasa da kasa sun ba da nasu shawarwari.

Da farko, a sanya marufin baki da hanci yadda ya kamata. Sanya marufin baki da hanci, hanya ce da ta dace da hana yaduwar annobar ta COVID-19. Amma a lokacin zafi, sanya marufin baki da hanci kan haddasa matsalar lafiya sakamakon tsananin zafi. Kwararrun sun ba da shawarar cewa, idan ana kasancewa a waje, kuma ana ba da tazara a tsakanin juna yadda ya kamata, to babu bukatar sanya marufin baki da hanci, musamman ma in ana motsa jiki a wajen daki. Amma idan ana cikin wuraren da aka samu cunkuson mutane, musamman ma a wuraren taruwan jama'a ko kuma ba a ba da tazara a tsakanin juna yadda ya kamata ba, to dole ne a sanya marufin baki da hanci. Ana iya sanya marufin baki da hanci mara kauri a lokacin zafi.

Na biyu kuma, a yi amfani da na'urar sanyaya daki ta hanyar da ta dace. Yin amfani da na'urar sanyaya daki yana iya kare mu daga tsananin zafi. Idan ba a yi amfani da na'urar sakamakon damuwar yaduwar annobar ba, to zai haddasa matsalar lafiya sakamakon tsananin zafi. Amma idan ana amfani da na'urar fiye da yadda ake bukata, za a raunana karfin garkuwar jikin dan Adam, ta haka mutane suna saukin kamuwa da cuta. Kwararrun sun bayyana cewa, dole ne a kashe kwayoyin cuta cikin na'urar sanyaya daki yadda ya kamata, kuma ya fi kyau a tabbatar da zafin dakin ya wuce digiri 26. Sa'an nan kuma ya fi kyau a rika bude tagogi domin shigar da iska. Idan an yi amfani da manyan na'urorin sanyaya daki a wuraren taruwan jama'a da kuma wuraren aiki, dole ne a yi amfani da su da kuma daukar matakan dakile da kandagarkin annobar yadda ya kamata.

Na karshe kuma, a sa kulawa kan wadanda suke saukin kamuwa da annobar. Tsoffin da shekarunsu suka wuce 65 da haihuwa suna saukin kamuwa da annobar ta COVID-19 da matsalar lafiya sakamakon tsananin zafi. Wadanda suka dade suna fama da ciwon sukari, matsalar kiba da cututtuka a huhu, koda, magudanar jini a zuciya, da 'yan kwadago da ke aiki a waje, ma'aikatan jinya, ma'aikatan ba da hidimomin al'umma, da masu juna biyu, zai fi kyau su dauki matakin ba da kariya yadda ya kamata.

Haka zalika, kwararrun sun ba da shawarar cewa, kamata ya yi al'umma su magance fita waje a lokacin tsananin zafi, su je wurare masu sanyi tare da shan isasshen ruwa yayin da suke aiki a waje. A tabbatar da sanyin wurin kwana da kuma wurin aiki. A rika yin mu'amala da masu saukin kamuwa da annobar wadanda aka killace su ko kuma wadanda suke zama da kansu. Idan sun gamu da matsalar lafiya sakamakon tsananin zafi, sai a ba su taimako kan lokaci. A tabbatar da ganin ma'aikatan jinya da masu ba da hidimomin al'umma wadanda suke sanye tufafin kariya suna aiki a wurare masu sanyi. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China