Kwanan baya, cibiyar bai wa matasa hidimar shari'a da ba da shawara kan tunani ta Beijing ta gudanar da wani kwarya-kwaryar bincike kan matasa kimanin dubu 100 a duk fadin kasar Sin, inda aka nuna cewa, barkewar annobar cutar numfashi ta COVID-19 ta haifar da babbar illa ga tunani da ma zaman rayuwar matasa
Sakamakon binciken ya nuna cewa, kusan rabin matasa da aka gudanar da binciken a kansu suna ganin cewa, ba sa jin dadi, sun ji tsoro, kuma hankalinsu bai kwanta ba. Kana kusan kashi 1 cikin kashi 3 daga cikin matasan sun ce, ko da yaushe suna amfani da wayar salula. Sa'an nan kimanin kashi 10 cikin kashi dari sun ce, ba sa kome sai wasa, sannan suna samun matsala da iyalansu sakamakon yadda suke wasa da shiga wayar salula.
Dangane da wannan, Zhang Chuji, wata likita ce da ke aiki a asibitin Tiantan na Beijing ta fada mana cewa, "barkewar annobar ta COVID-19 ta haifar da babbar illa ga tunani da ma rayuwar matasa. Idan ba a warware matsalolin tunanin matasa da suka gamu da su yayin da ake yaki da annobar ba, to watakila matsalolin za su dade suna addabar matasan a fannonin karatu, zaman rayuwa da yin mu'amala da mutane."
Hakika dai, barkewar annoba ta dade tana adabar tunanin matasa. Alal misali, watakila idan matasa sun gamu da yanayi na kaduwa mai tsanani, hakan zai iya saka su kamu da larurar damuwa da kansu biyo bayan wata masifa ko "post-traumatic stress disorder" wanda ake wa lakabi da "PTSD" a takaice. Yaduwar annobar tana rika ta da hankalin matasa, lamarin da yake saukin haifar da rikici a tsakanin iyaye da 'ya'yansu. Bayan da wasu matasa suka koma makaranta, kwazonsu ya yi kasa, sun fuskanci babban matsin lamba fiye da kima. Sakamakon yin karatu a gida cikin dogon lokaci, ya sa wasu matasa ba su saba da yin karatu a makaranta ba, ba su iya tashi da wuri da safe, barci ba ya isar su. Haka zalika, bayan da wasu suka koma makaranta, sun ji tsoron yin mu'amala da abokan karatunsu da suka fito daga wuraren da annobar ta taba yin kamari. Huldar da ke tsakaninsu da abokan karatunsu ta rauni. Don haka ya zama tilas dauki matakai don yaki da matsalolin tunani cikin dogon lokaci sakamakon barkewar annobar.
Likitar ta ba da shawarar cewa, ya kamata a taimaka wa matasa su fahimta su kuma amince da abubuwan da suka ji, kowa yana bakin ciki ko fushi kamar yadda yake yin farcin ciki. Suna iya mai da hankali kan karatu, aiki, da iyalai. Suna kuma iya kyautata kwarewarsu ta tafiyar da harkokinsu da kansu. Ban da haka kuma, kamata ya yi iyayen matasa su kara yin cudanya da 'ya'yansu, su tattauna abubuwan da 'ya'yansu suka ji tsoro ko su ke damunsu. Ba shakka dole ne iyayen su mai da hankali kan lafiyar tunaninsu, kada su rika tsorata 'ya'yansu. Idan sun gano 'ya'yansu sun gamu da babbar matsalar tunani, ya zama tilas su kai su wajen likita a kan lokaci domin samun taimako. (Tasallah Yuan)