Zhang Chuji, wata likita ce da ke aiki a dakin jinyar gaggawa a asibitin Tiantan na Beijing ta yi karin bayani da cewa, idan zafin jikin kananan yara bai wuce digiri Celsius38.5 ba, za a iya jika tawul ko tsumma a ruwa mai dumi-dumi, bayan an matse shi, sai a goge jikinsu don rage zafin jikin. Amma idan jikin kananan yara yana da zafi sosai, har ya wuce digiri Celsius38.5, sa'an nan kuma, ba su jin dadi, har ba su da karfi, to ya zama dole su sha maganin zazzabi a kan lokaci.
Amma abun da ya kamata a lura da shi shi ne bayan da kananan yara suka sha maganin zazzabi, amma zazzabin bai sauka ba, kamata ya yi su sake shan maganin bayan ko wadanne awoyi 4 zuwa 6 a kalla. Madam Zhang ta kara da cewa,nan da nan maganin yake saukar da zazzabin da kananan yara suke fama da shi. Idan har kananan yaran suka shafe dauki kwanaki fiye da 3 a jere suna fama da zazzabi, kuma zazzabin ya ki sauka, zafin jikinsu bai ragu ba, ko kuma ba su da kuzari, ba su son cin abinci, har suka rame, ya zama tilas a kai su asibiti don ganin likita cikin hanzari.
Likitar ta yi gargadi da cewa, yayin da ake kokarin rage zafin jikin kananan yara, ana iya jika wani abu mai kama da tawul da ruwa madaidaici, babu zafi kuma babu sanyi, bayan an matse shi, sai a goge jikinsu da shi, ya dace a tabbatar cewa, zafin ruwan ya wuce digiri Celsius 32 amma bai kai 34 ba. Haka kuma, yayin da ake goge musu jikin, kada a shafa a kirjinsu, cikinsu, bayan wuyansu, tafin kafa da sauran sassan jikinsu wadanda ba za su iya jure sanyi ba. Amma ana iya dan tsawaita lokaci yayin da ake ana goge hamatarsu, cikin gwiwar hannu, da gwiwar kafa da wurin jiki inda kaluluwa take.
Likitan ta ci gaba da cewa, kada a shafa wa kananan yara man da aka hada na sinadarin barasa a jikinsu ba, saboda fatar kananan yara na da laushi sosai, watakila zai iya jin zafi a jikinsu. Har ila yau kuma dole ne a tabbatar da kananan yara masu fama da cutar mura su sha isasshen ruwa, musamman ma yayin da suke fama da tsananin zafi, saboda su zuciyarsu tana bugawa da sauri, su kan yi gumi da yawa, don haka su kan rasa ruwa da yawa. Idan sun sha isasshen ruwa, nan da za su yi fitsari, ta yadda za su warke cikin gajeren lokaci. (Tasallah Yuan)